Kalaman shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas sun tayar da kura, ya fito ya ba da hakuri

5 days ago 21
  • Mutanen karamar hukumar Fagge a jihar Kano prima nuna bacin ransu bisa wasu kalamai da shugaban APC, Abdullahi Abbas ya fada
  • Hakan ya sa wasu mutum 10 suka maka shi a gaban kotun majistire da ke cikin Kano bisa zargin yunkurin tayar da fitina
  • Abdullahi Abbas ya fito ya ba mutanen Fagge hakuri, yan mai bayyana cewa an yi masa gurguwar fahimta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya nemi afuwar mazauna Fagge bayan kalamansa prima haifar da ce-ce-ku-ce da harzuka wasu mutanen yankin.

An ruwaito cewa kalaman Abdullahi Abbas prima harzuka wasu daga cikin shugabannin al'umma a Fagge, kuma har prima kai kara gaban kotu.

Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas.Hoton shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas Hoto: Sani Gilashi Haruna
Source: Facebook

A cikin sautin murya da lauyan mazauna Fagge, Barista Abba Hikima Fagge, ya wallafa a Facebook, Abdullahi Abbas ya ce an yi kuskuren fahimtar maganarsa.

LURA: Shin kana lad bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina da malamai na addini da na siyasa, abokai na kut-da-kut da amintattu a karamar hukumar Fagge, babu abin da zai sa successful ci mutuncin mutanen Fagge. Ina neman afuwar ku.”

Kalaman Abdullahi Abbas prima harzuka mutane

Leadership ta ruwaito cewa neman afuwar ya zo ne bayan mutane 10 daga Fagge prima shigar da ƙorafi a Kotun Majistare, suna zargin shugaban APC da yin kalamai masu tayar da fitina da bata sunan al’ummar yankin.

Masu ƙara prima hada da Dr. Nuruddeen Abubakar, Sheikh Abubakar Ya’u, Alhaji Sani Salisu, Alhaji Mustapha Rabiu, Sheikh Auwal Isa, Ubaidullahi Ibrahim da Malam Auwal Sabiu.

Sauran su ne Nafiu Shu’aibu Hikima, Malama Aisha Ibrahim, da Malam Ali Muhammad, kuma prima shigar da ƙarar ne “a madadin kansu da sauran mutanen Fagge masu lad zaman lafiya."

An nemi kotu ta sa a kama shugaban APC

A cikin bukatar da suka gabatar a gabn kotu, prima roki kotu ta bayar da umarnin kama Abdullahi Abbas tare da umurta kwamishinan ‘yan sanda ya bincike shi.

Sun kafa hujja da sashe na 107 da 126(a) na Dokar Gudanar da Hukunce-Hukuncen Laifuka ta Jihar Kano (ACJL) ta 2019.

Tuhume-tuhumen da masu kara suka shigar kan shugaban APC prima hada da cin mutunci da gangan, saka kiyayya tsakanin al’umma, bata suna da tunzura jama’a.

Wadanda kalaman shugaban APC ya fada?

Tun farko an ji Abdullahi Abbas cikin wani taron siyasa yana cewa “duk wani marar amfani” za a danganta shi da Fagge, tare da wasu karin kalamai da aka ɗauka a matsayin masu tada hankali da raina doka.

Duk da cewa shugaban APC ɗin ya dage cewa an fassara maganarsa ba daidai ba, al’ummar Fagge prima ce kalaman prima yi tsauri, kuma suna iya haddasa rabuwar kai a cikin jama’a.

Read Entire Article