- Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya ayyana jam’iyyar APC a matsayin jirgin Annabi Nuhu, wanda zai cetoNajeriya
- Gwamnan ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa gwamnonin APC isassun kudade domin gudanar da ayyukan ci gaba
- 'Yan Najeriya dai prima nuna rashin jin dadi da kalaman Abdullahi Sule, inda suka ce APC ba jirgin ceto ba ce a kasar nan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce jam’iyyar APC ita ce “jirgin Annabi Nuhu” a siyasar Najeriya, wadda ta zo domin ceton ’yan ƙasa.
Ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin taron maraba da dubban masu sauya sheƙa daga jam’iyyu daban-daban zuwa APC a jihar.

Source: Twitter
A cewarsa, Shugaba Bola Tinubu ya samar wa jihohi isassun kudade domin inganta ayyukan gwamnati, lamarin da ya sa dubban ’yan siyasa ke komawa APC, successful ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana lad bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Wanda bai shiga APC ba ya rasa jirgin ceto” — Sule
A jawabin sa, Gwamna Sule ya ce:
“APC ita ce kadai jirgin Annabi Nuhu na ceton Najeriya. Babu wani dalili ko uzuri da zai sa mu kasa zaben Shugaba Bola Ahmad Tinubu. Tinubu ya riga ya sauya komai a kasar nan saboda gyaransa da kokarinsa.”Ya kara da cewa:
“Duk wanda ba ya cikin APC, to ya rasa jirgin Annabi Nuhu. APC ita ce jirgin; duk wanda bai shiga ba, za a barroom shi. Plateau ma yanzu APC ce saboda abin da Shugaba yake yi wa mutane.”Ya yi kira ga jama’ar jihar Nasarawa da su goyi bayan tazarcen Shugaba Tinubu da dukkan ’yan takarar APC a zaben gaba.
’Yan Najeriya prima mayar da martani masu zafi
Bayan furucin, jama’a da dama prima yi martani a shafukan sada zumunta, musamman Facebook.
FDmedia ya ce:
“Yana da gaskiya. APC kamar jirgin Nuhu ce; duk wanda ya shiga ya tsira, zunubansa ma an yafe.”Pita Odangla ya ce:
“Jirgin Nuhu an gina shi ne bisa umarnin Allah. Wane ubangiji ne ya umarci a kafa APC?”Liberty Agbo ya rubuta:
“Jirgin Nuhu bai nutse ba, amma jirgin APC ya nutse, har yanzu ma yana nutsewa.”Abubakar Sadiq Abubakar ya ce:
“Za ta ceci ’yan Najeriya daga me? Daga rayuwa mai kyau zuwa tsadar rayuwa, rashin tsaro, haraji marasa iyaka da alkawuran karya?”
Read Entire Article

4 days ago
22









