- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura Dr. Abiodun Essiet zuwa jihar Plateau domin jagorantar tattaunawar zaman lafiya
- Dr. Essiet ta gudanar da tarurruka a Barkin Ladi da Jos, inda ta gana da shugabannin addini, sarakuna da kungiyoyin matasa
- An samu gagarumin ci gaba lokacin da aka warware rikicin da ya faru tsakanin manomi David Toma da wasu makiyaya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura Dr. Abiodun Essiet a matsayin jakadiyarsa zuwa Plateau domin karfafa sulhu da dawo da zaman lafiya tsakanin al’ummomin jihar.
Dr. Essiet, ta kasance tana aiki ne a matsayin babbar mai taimakawa shugaban kasa kan huldar jama’a a yankin Arewa ta Tsakiya.

Source: Twitter
Wakiliyar Tinubu ta isa jihar Filato
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a ranar 16 Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana lad bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Onanuga ya sanar da cewa Dr. Essiet ta kwashe kwanaki biyu a jihar Filato tana gudanar da tattaunawa da shugabanni daban-daban.
"Ta gana da manyan limaman Kirista da shugabannin al’ummar Fulani Miyetti Allah, domin samar da hanyoyin fahimtar juna da karfafa zaman tare tsakanin manoma da makiyaya."- Bayo Onanuga.
Wakiliyar Tinubu ta gana da al'umomin Jos
Ziyarar ta kai ga gudanar da taron dandalin tattaunawa a Jos, inda wakilai daga kananan hukumomi daban-daban, sarakunan gargajiya, shugabannin mata da matasa suka hallara domin tattauna hanyoyin karfafa tsarin zaman lafiya a matakin al’umma.
A Barkin Ladi, Dr. Essiet ta kai ziyara wajen Reverend Ezekiel Dachomo, shugaban Regional Church Council (RCC), inda suka tattauna rawar shugabannin addini wajen kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Sanarwar ta kuma ce"
"Dr. Essiet ta kuma yi jawabi ga wasu zawarawa tare da isar da sakon Shugaba Tinubu na sulhu da hada kan kabilu a jihar Filato."Dr. Essiet ta gana da shugabannin Fulani a Barkin Ladi domin karfafa tattaunawa da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma, tare da tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na kara karfafa hadin kai.
An jaddada kudurin Tinubu na zaman lafiya a Filato
Daga nan ta jagoranci taron horaswa kan kafa tsarin zaman lafiya na al’umma a kananan hukumomi 17 na jihar.
Ta kuma yi ganawar sirri da al’ummar Irigwe, kungiyar Miyetti Allah, da kungiyar matasan Bassa LGA domin tattauna matakai na dorewar zaman lafiya da aikin kwamitin sulhu mai mutum 17.
Dr. Essiet ta jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar ganin an samu zaman lafiya, adalci da hadin kai a yankin Arewa ta Tsakiya.
Ta bayyana cewa tsarin zaman lafiya na garuruwa na taka muhimmiyar rawa wajen gina daɗaɗɗen zaman lafiya ...

4 days ago
17









